in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
JKS za ta kira wani taro daga ranar 9-12 ga watan gobe don zurfafa shirye-shiryen yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje
2013-10-29 17:45:58 cri
Taro karo na uku na JKS na cikakken zama na 18 na kwamitin tsakiya za'a yi shi ne a tsakanin ranaikun 9 zuwa 12 ga watan gobe na Nuwamba a birnin Beijing, fadar gwamnatin kasar Sin, kamar yadda sanarwar da hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar ta fitar a ranar Talatan nan.

Sanarwar ta fito ne bayan da s hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar ta yi wani taro da Shugaban kasar Xi Jinping ya jagoranta a matsayinsa na babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar don nazarin yadda za'a zurfafa shirye-shiryen yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje da ake yi.

A lokacin taron, an saurari rahotanni game da ra'ayin da aka samo daga ciki da wajen jam'iyyar a kan shawarwarin kwamitin tsakiya na jam'iyyar a kan manyan bukatun da suka shafi zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje da ake shirin yi.

Shi dai wannan daftarin kuduri za'a gabatar da shi ne a taro karo na uku na JKS na cikakken zama na 18 na kwamitin tsakiya domin masa gyara.

Yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje wata dama ce ta wani babban kokarin da Sinawa suke yi a karkashin mulkin JKS a sabon karni. Zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje na bukatar inganci da ci-gaba na walwala irin na kasar Sin, kamar yadda sanarwar tayi bayani.

Ya kamata karfafa tare da inganta shugabancin JKS, tare da ba da dama ga jam'iyyar da ta aiwatar da cikakken ikonta, ta yadda za a iya tabbatar da samun nasarar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, in ji sanarwar.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China