in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisun kasar Amurka sun zartas da shirin samar da kudi na wucin gadi
2013-10-17 16:04:51 cri

Majalisun dattawa da na wakilan kasar Amurka sun zartas da wani shiri a ran 16 ga wata, inda ya baiwa gwamnatin tarayyar damar samun kudi na gajeren lokaci, tare kuma da kara yawan bashin kudin da za ta iya karba.

A wannan rana da dare, majalisar dattawan kasar ta zartas da shirin bisa kuri'un amincewa 81, da na kin amincewa 18, wanda mambobin majalisun biyu sun yi hadin kai ne domin gabatar da shi da zummar dawo da ayyukan ma'aikatan gwamnati da kaucewa fadowar kasar cikin rikicin bashi. A wannan rana da dare kuwa, majalisar wakilai ita ma ta zartas da kudurin.

Bisa shirin da aka zartas, hukumomi daban-daban na gwamnatin za su samu kasafin kudin tafiyar da harkokinsu har zuwa ran 15 ga watan Jarairu na shekarar 2014 mai zuwa, a sa'i daya kuma, an kara wa'adin gabatar da basusukan kasar zuwa ran 7 ga watan Fabrairu na shekarar 2014.

Bisa tsarin dokokin kasar, za a kaddamar da wannan shiri bayan da majalisun biyu sun zartas da shi, sa'a nan shugaban kasar ya sa hannu. Shugaba Barack Obama ya furta a daren ranar Laraba cewa, zai kaddamar da shirin da zarar ya sa hannu domin a hanzarta bude ma'aikatun gwamanati. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China