Cibiyar "Grant Thornto International" ta kasar Amurka ce ta yi binciken kan yadda yankuna na kasashe 50 suke bunkasa tattalin arzikinsu a shekarar 2013 ta fannoni biyar, wato yanayin da masana'antu ke ciki wajen gudanar da harkokinsu, saurin bunkasa tattalin arziki, kimiyya da fasaha, kwadago da kuma yadda ake samun rance.
Bisa wannan ma'aunin da cibiyar "Grant Thornto International" ta tsara, kasar Sin na kan matsayi na uku a shekarar 2013 bayan da ta bar matsayi na 17 a shekarar 2012.
Bisa wannan binciken da aka yi, an ce, dalilin da ya sa kasar Sin ta samu ci gaba sosai shi ne tana da karfi sosai wajen bunkasa kimiyya da fasaha. (Sanusi Chen)