Li Jinzao ya ce, a matsayin wata kasa mai tasowa da yawan mutanenta ya kai matsayin farko a duniya, Sin na kokarin kawar da masu radadin fatara, kuma tana kokarin ba da gudummawarta ga tattalin arzikin duniya ta hanyar samun bunkasuwar kanta.
Ya ce Sin za ta ci gaba da yin amfani da tsarin yin hadin gwiwa tsakanin bangarori da yankuna daban-daban, da kuma ba da taimako gwargwadon karfinta domin taimakawa sauran kasashe masu tasowa wajen kafa wasu manyan ababen more rayuwa dangane da sha'anin ciniki bisa bukatunsu, sa'an nan tana yin hadin kai a fannin kimiya da fasaha da kuma da ba horaswa ta yadda za a taimakawa kasashe masu tasowa wajen inganta kwarewarsu a fannin ciniki, har ma da ci gaba da cika alkawarinta na buga harajin sifiri kan wasu hajjoji, da kara shigar da kayayyaki daga kasashen da suka fi fama da talauci a duniya. (Amina)