in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira da a dauki matakan sa ido ga bunkasar tattalin arzikin duniya
2013-10-11 10:21:27 cri

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wang Min, ya yi kira ga MDD da gamayyar kasashen duniya, da su dauki matakan kulawa da tattalin arzikin duniya, domin tabbatar da ci gaba da bunkasarsa.

Wang Min, wanda ke tsokaci gaban mambobin kwamiti na biyu, dake karkashin babban zaman majalissar karo na 68, ya ce, daukar wannan mataki ne kawai zai wanzar da burin da ake da shi, na ci gaban tattalin arzikin kasashe masu tasowa.

Wakilin kasar ta Sin ya kara da cewa, daukar matakan samar da ci gaba na bai daya tsakankanin kasashen duniya, ta yadda ci gaban wasu ka iya karfafar na sauran kasashe, muhimmin mataki ne da ya dace MDD ta jagoranci tabbatar sa.

Daga nan sai ya nanata bukatar da ake da ita na samar da kyakkyawan yanayin bunkasuwa, da zai haifar da cigaban tattalin arzikin duniya daga dukkanin fannoni. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China