Lami ya ce, tabbatar da samun karuwar tattalin arziki yadda ya kamata zai kawo alheri ga kasashen duniya.
Yayin da aka tabo maganar kiki-kakar cinikin da ke tsakanin kasar Sin da wasu kasashen kungiyar EU a cikin watannin da suka gabata, Lamy ya ce, duk inda ake cinikayya, ba za a rasa kiki-kakar da ke faruwa ba. Ana iya cewa, kasar Sin da kungiyar EU, abokan cinikayya ne mafi girma a duniyar yanzu, ko wace rana, su kan yi cinikin da darajarsa ta zarce kudin Euro biliyan 1. sabo da haka, za a yi amfani da tsarin shiga tsakani na WTO don warware wannan batu.
Lamy ya ce, yin ciniki ba tare da shingaye ba, ya zama hanya mafi kyau da za a bi wajen sa kaimi ga samun karuwar tattalin arziki. Haka kuma, darikar kare harkokin cinikin kasashe za ta kawo cikas ga batun farfado da tattalin arzikin duniya. Don haka, shugabannin kasar Sin da na kungiyar EU sun amince sosai da muhimmancin hakan.(Bako)