Madam Lagarde ta bayyana cewa, a halin yanzu akwai kungiyoyi uku a duniya a fannin bunkasuwar tattalin arziki. Kasashen da suka fi samun ci gaban tattalin arziki sun zama rukuni na farko, wasu kasashe kamar Amurka, Sweden, da Switzerland sun fara samun farfadowar tattalin arziki, inda suka zama rukuni na biyu. Su kuma kasashen yankuna masu amfani da kudin Euro da kasar Japan suna kokarin neman hanyar raya tattalin arziki, don haka suna cikin rukuni na uku.
Bugu da kari, Madam Lagarde ta ce, kasashen duniya suna cikin mawuyacin hali a yanzu, inda ta jaddada cewa, wajibi a dauki matakan tsuke bakin aljihu, domin ita ce kadai hanyar warware matsalar. (Zainab)