in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin kiyaye muhalli zai taimakawa kasashe masu tasowa
2013-05-09 16:41:16 cri

Hukumar tsara shiri kan muhalli ta MDD wato UNEP ta ba da wani rahoto a ran 8 ga wata cewa, tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba zai taimaka wajen raya tattalin arzikin duniya, don haka ya kamata kasashe masu tasowa su yi amfani da zarafi mai kyau domin samun bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa.

Wannan rahoto mai jigo "hanyar da za a bi, kalubale da zarafi da ake fuskanta wajen raya tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba" ya amince da taimakon da cinikayyar dake tsakani kasa da kasa take bayar wa wajen gaggauta bunkasuwar tattalin arzikin duniya. Ban da haka, rahoton ya yi nazari kan yadda irin wannan tattalin arziki na ba tare da gurbata muhalli ba ke zarafi ga kasashe masu tasowa.

Rahoton ya nuna cewa, ya zuwa yanzu, kasuwar samun bunkasuwar tattalin arziki mai dorewa na kara habaka, a sa'i daya kuma, ana samun karin kasuwanni na kayayyakin da aka sarrafa ba tare da gurbata muhalli ba, abin da ya samarwa kasashe masu tasowa dama da zarafi masu kyau wajen raya tattalin arziki a fannoni daban-daban da samun moriya mai daraja. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China