in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar IMF ta yi kira ga kasashen duniya da su kara daidaita manufofinsu
2013-10-11 16:45:04 cri

Shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF Christian Lagarde ta nuna a jiya Alhamis 10 ga wata cewa, yauzu saurin karuwar tattalin arzikin duniya ya ragu, ya kamata kasashen duniya su kara daidaita hadin gwiwa a fannin manufofi saboda ganin cewa suna alaka da juna ta fuskar tattalin arziki da kasuwar hada-hadar kudi, ta haka zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin duniya.

Christian Lagarde kuma ta bayyana a gun wani taron manema labaru da aka yi kafin taron shekara-shekara da IMF da bankin duniya su kan yi na cewa, ya kamata, kasa da kasa sun yi sulhu da kuma hadin kai yayin da suke tsayar da manufofin kudi, tare kuma da sa kaimi ga kwakwarima da za a yi a fannin tsare-tsare da hada-hadar kudi.

An ba da labari cewa, IMF da bankin duniya sun kira taron shekara-shekara na shekarar 2013 daga ran 11 zuwa 13 ga wata a birnin Washington. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China