A wannan rana, darektan kula da harkokin yankin gabas ta tsakiya da na tsakiyar Asiya na IMF Masood Ahmed ya isa kasar Masar tare da wata tawagar kwararru, inda suka gana da firaministan kasar. Bayan ganawarsu, Masood Ahmed ya bayyana cewa, zai ba da goyon bayansa ga kasar Masar wajen samar canje-canje ta fuskar tsarin tattalin arzikinta, ta yadda za ta iyar fuskantar kalubalolin da kasar take cin karo a bangaren tattalin arziki. Haka zalika, cikin makonni masu zuwa, tawagar kwararrun asusun ba da lamuni na IMF za ta yin hadin gwiwa tare da gwamnatin kasar Masar wajen gudanar da rancen kudi.
Tun lokacin da aka samu barkewar rikice-rikice a kasar Masar a farkon shekarar 2011, yanayin tattalin arzikin kasar ya tabarbare sosai, yayin da yawan ajiyar kudin musanya ta kasar ya ragu matuka, wanda aka kiyasta a halin yanzu ga dalar Amurka biliyan 13.5 kawai, lamarin da kila zai kawo wa tattalin arzikin kasar barazana. Don gane haka, gwamnatin kasar Masar take bukatar cimma nasarar shawarwarin da ke tsakaninta da IMF sosai, ta yadda za ta samu tallafin IMF na rancen kudin kusan dalar Amurka biliyan 4.8 don fuskantar da kalubalolin tattalin arziki. Bugu da kari, bangarorin biyu sun taba kulla wata yarjejeniya a watan Nuwamba na shakakar bara, amma gwamnatin kasar Masar ta kasa kawo canje-canje kan tattalin arzikinta a sakamakon tashe-tashen hankali da suka barke a cikin kasar. (Maryam)