in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukunta a Somaliya sun yabawa asusun bada lamuni na duniya
2013-04-14 16:29:04 cri

Mahukuntan kasar Somaliya, sun yabawa amincewar da asusun bada lamuni na duniya IMF ya yiwa halascin gwamnatin kasar, matakin da zai baiwa kasar damar cin basussuka daga bankuna da cibiyoyin bada lamuni na kasa da kasa, tare da samun tallafin kwararru, da kuma shawarwari kan harkokin da suka shafi tsare-tsaren tattalin arziki.

Wata sanarwa da ta fito daga ofishin firaministan kasar Abdi Farah, ta bayyana wannan mataki a matsayin wata kyakkyawar hanya, da za ta baiwa kasar damar aiwatar da tsare-tsaren ci gaba, bayan ta shafe shekaru sama da 20 da rasa wannan dama.

Sanarwar ta kuma kara da bayyana shirin mahukuntan kasar, na amfani da wannan dama, domin nunawa asusun na IMF, dama ragowar duniya irin burin da suke da shi, na cimma nasarorin bunkasa kasar, ta hanyar zage dantse da aiki tukuru.

Koda yake dai wannan dama na da amfani matuka ga kasar ta Somaliya, a hannu guda bankin na IMF yace ba za a fara baiwa kasar rance ba, har sai ta biya bashin da yake binta, wanda yawansa ya kai dalar Amurka miliyan 352. Baya ga Asusun na IMF, shi ma babban bankin duniya na bin Somaliyar kimanin dalar Amurka miliyan 250.

Wannan dai batu na amincewa da Somaliyan ta samu, ya biyo bayan sanarwar da asusun na IMF ya fitar a ranar Jumma'ar da ta gabata, a kuma dai dai lokacin da gwamnatin kasar ke shirin gudanar da taron masu ruwa da tsaki, domin kamo bakin zaren habaka ci gaban kasar, taron da kasar Birtaniya zata dauki nauyin gudanarwa a farkon wata mai zuwa.

Tuni dai mahukuntan kasar suka bayyana cewa, batun biyan bashin da ake bin kasar, zai kasance cikin muhimman batutuwan da za a tattauna a taron mai zuwa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China