in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asusun IMF ya ce tsarin kudi na duniya yana fuskantar manyan gyare-gyare
2013-10-10 16:18:25 cri

Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya gabatar da rahoton harkokin kudi na duniya a ran 9 ga wata, inda aka bayyana cewa, yanzu tsarin kudi na duniya yana fuskantar manyan gyare-gyare, bisa halin da ake ciki na fuskantar sababbin kalubaloli, ana iyar kuma ganin cewa, kasar Amurka tana shirin daina manufofinta na kara zuba kudi a kasuwanni, yayin da kasar Japan take cikin jinkirin tabbatar da kyakkyawan sakamakon da manufar Abenomics da firayin minista Shinzo Abe ya gabatar, kuma sababbin kasuwanni na samun raguwar bunkasuwa a lokacin da ake kara zaman dar-dar a duniya.

A wannan halin da tsarin kudin duniya ke ciki, Asusun IMF yana ganin cewa, sababbin kasuwanni suna fuskantar kalubalen yanayin duniya dake kara canzawa, kuma yawan karuwar tattalin arzikinsu ya ragu, sabo da haka, ya kamata wadannan sababbin kasuwanni su daidaita matsalolin da suke fuskanta a fannin hada-hadar kudi da tattalin arziki, ta yadda za a iya samun bunkasuwarsu cikin adalci da karko.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China