Wani babban jami'in asusun kudin duniya IMF dake ziyarar aiki a kasar Mozambique, ya nuna jurewar kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara ta fuskar tattalin arziki da hasashen bunkasuwa ta kashi 5.4 cikin 100 cikin wannan shiyya a shekarar 2013.
Mista David Lipton, mataimakin darektan IMF, ya bayyana cewa, wannan shiyya ta samu bunkasuwa da kashi 5.1 cikin 100 a shekarar da ta gabata, kana wannan adadi zai iyar cimma kashi 5.4 cikin 100 a shekarar 2013 da kuma kashi 5.7 cikin 100 a shekarar 2014, a yayin da aka kiyasta tattalin arzikin duniya zuwa kashi 3.3 cikin 100 a wannan shekarar da muke ciki da kuma kashi kashi 4 cikin 100 a shekara mai zuwa.
Game da tattalin arzikin kasar Mozambique, mista Lipton ya shawarci kasar da ta ba da karfi wajen cike raguwar bukatun kasashen Turai ta hanyar karfafa dangantakarta tare da tattalin arzikin kasashe masu tasowa.
A shekarar 2012, kasar Mozambique ta samu bunkasuwa da kashi 7.4 cikin dari. A shekarun baya bayan nan, kasar ta zama muhimmiyyar kasa a fagen kasuwannin duniya na makamashi.
Manyan kamfanonin makamashi na kasashen Turai da Amurka na hakar iskan gas a gabar wannan kasa. Haka kuma gundumar Tete dake arewacin kasar na kunshe da daya daga cikin gandun arzikin karkashin kasa na kwal a duniya. (Maman Ada)