Asusun bayar da lamuni na duniya wato IMF ya bayar da sabon rahoto kan hasashen bunkasuwar tattalin arzikin duniya a ran 8 ga wata, inda ya rage hasashen ya yi game da bunkasuwar tattalin arzikin duniya a cikin shekarar bana da shekara mai zuwa, kuma asusun ya yi gargadi cewa, a halin da muke ciki yanzu, tattalin arzikin duniya bai samu bunkasuwa cikin sauri ba, kuma akwai yiyuwar kara raguwa.
Rahoton ya yi hasashe cewa, yawan karuwar tattalin arzikin duniya a shekarar bana da shekara mai zuwa zai kai kashi 2.9 bisa dari da kuma kashi 3.6 bisa dari, hasashen da aka rage zuwa kashi 0.3 bisa dari da kuma kashi 0.2 bisa dari. Rahoton ya yi hasahen cewa, yawan karuwar tattalin arzikin da kasar Sin za ta samu a shekarar bana da shekara mai zuwa zai kai kashi 7.6 bisa dari, da kuma kashi 7.3 bisa dari, wanda da zai ragu da kashi 0.2 bisa dari da kuma kashi 0.4 bisa dari idan aka kwatanta hasashen da aka yi a watan Yuli na shekarar bana.
Rahoton ya ce, ana samun canji kan hanyoyin karuwar tattalin arziki a duk duniya, kasashe masu ci gaba suna ta samun karuwa a kai a kai, amma kasashe da ke samun saurin bunkasuwa a shekarun da suka gabata suna fuskantar kalubaloli a fannonin raguwar bunkasuwa da kuma lalacewar kasuwannin kudi a duk duniya.(Danladi)