Bisa kididdigar da hukumar kiwon lafiya ta kasar Masar ta fitar da kuma labarin da kafofin watsa labaru na kasar suka bayar, an ce, a yankin Gabas da jihar Port Said, magoyan bayan Morsy sun yi dauki ba dadi tare da mazaunan jihohin, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3 baya ga mutane fiye da 10 da suka ji rauni. Kana a jihar Alexandria, da Ad Daqahliyah da sauran jihohin kasar, an samu tashe-tashen hankula a tsakanin magoyan bayan Morsy da masu adawa da su, wadanda ya haddasa raunatar mutane fiye da 10.
Bugu da kari, magoyan bayan Morsy sun yi zanga-zanga a manyan filaye da hanyoyin motoci a birnin Alkahira. Kana darurukan mutane daga cikin masu zanga-zangar sun kewaye wani ofishin 'yan sanda dake Ain Shams, suna masu bukatar da a saki membobin kungiyar 'yan uwa musulmi dake tsare a ofishin. (Zainab)