A daya bangare kuma, a ranar 3 ga wata, wata kotun kasar Masar ta yanke hukuncin hana gidan telebijin na Al Jazeera da sauran kafofin telebijin Musulunci 3 watsa shirye-shiryensu a kasar Masar. Haka kuma, kotun ta zargi wadannan kafofin telebijin da kawo baraka ga kasar. Ban da gidan telebijin na Al Jazeera, sauran kafofin sun hada da gidan telebijin da ke karkashin kungiyar 'yan uwa Musulmi ta kasar, da kafofin telebijin na Yarmuk da Al-Quds.
Ministan yada labaru na kasar Masar ya taba bayyana cewa, hana gidan telebijin Al Jazeera gabatar da shirye-shiryensu a Masar zai biya bukatun jama'a, tare da nuna cewa, gidan telebijin din Al Jazeera bai da lasinsin watsa shirye-shiryensu a kasar Masar.(Bako)