A wannan rana kuma, hukumar harkokin cikin gida ta Masar ta ba da sanarwar musunta labarin mutuwar Mohammed Badie. Tashar yanar gizo ta jaridar Al-Ahram ta rawaito kalaman hukumar tsaro cewa, mahukuntan sun riga sun tura wani rukunin likita zuwa gidan kurkuku na Tora domin ba shi jiyya. Kuma labarin ya kara da cewa, yanzu Mohammed Badie ya riga ya sami sauki.
A karshen watan Yuli, masu kai kara na Masar sun tuhumi Mohammed Badie da wasu sauran manyan jami'an kungiyar Muslim Brotherhood da laifin ta da zaune tsaye, kuma sun bukaci a tsugunar da su a gaban kotun manyan laifuka.
A ran 20 ga watan Agusta, 'yan sandan Masar sun cafke Mohammed Badie mai shekaru 70 a duniya a birnin Nasr dake arewa maso gabashin birnin Alkahira. Daga bisani an tsare shi a gidan kurkuku na Tora dake kudancin birnin Alkahira. Kafin wannan, dansa mai shekaru 38 da haihuwa ya mutu cikin rikicin da aka yi a kusa da filin Ramses na wannan birni.(Fatima)