Kamfanin dillancin labaru na MENA na kasar Masar ya ruwaito hukumomin tsaron kasar na cewa, 'yan sandan kasar sun kama Gehad El-Haddad a wani gida dake birnin Nasr wanda ke arewa maso gabashin Alkahira, yayin da kuma aka kama wasu manyan jami'an jam'iyyar 'yan uwa musulmi, ciki har da Hossam Abu El-Bakr da Mahamoud Abu Zeid. A yanzu haka ana tsare da su a gidan kurkuku na Torah, don yi musu bincike kan zargin tayar da hankali da amfani da karfin tuwo, da yi wa masu zanga-zanga kisan gilla.
An ce, Gehad El-Haddad shi ne daya daga cikin muhimman kakakin jam'iyyar 'yan uwa musulmi a yayin da Mohamed Morsi ya rike kujerar shugabancin jam'iyyar na kasa, a lokacin kuma ya taba yin mu'amala da kafofin watsa labaru na kasashen ketare. (Bilkisu)