An hallaka Mohammed Abdullah dake tsagin magoya bayan Morsi ne a Tanta, garin dake yankin Gharbiya dake kusa da gabar kogin Nilu. Hakan kuma ya biyo bayan fitar dubban magoya bayan kungiyar 'yan uwa musulmi titunan yankunan kasar don gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da gwamnatin da sojojin kasar ke marawa baya, suna masu kira da a dawo da tsohon shugaban kasar Mohammad Morsi kan mukaminsa. Zanga-zangar da aka fara gudanarwa bayan kammala sallar Jumma'a ta yadu a sassa daban daban, ciki had da birnin Al-Kahira, da Giza, da gundumar Ramses da dai sauransu.
Manazarta dai na ganin wannan zanga-zanga na gwada irin yadda magoya bayan kungiyar ta 'yan uwa musulmi ke kokarin turjewa bukatar mahukuntan kasar, ta ganin sun kau da dukkanin nau'o'in tarzoma da jan- daga da masu adawa da gwamnatin rikon kwaryar ke nunawa.
Rikicin siyasar kasar ta Masar dai ya barke ne tun bayan hambarar da zababbiyar gwamnatin Mohammed Morsi a ranar 3 ga watan Yulin da ya gabata, wadda kuma ta sabbaba rasuwar daruruwan fararen hula, ciki had da magoya bayan kungiyar ta 'yan uwa musulmi, kungiyar da kuma mahukuntan kasar suka ba da umarnin cafke da dama daga jagororinta. (Saminu)