Kakakin shugaban kasar ya bayyana cewa, wannan kwamiti zai duba sabon daftarin tsarin mulkin kasar da za a bayar a ranar 8 ga wata. Bisa shirin da Shugaban Mansour ya sanar, an ce, za a kammala aikin dubawa cikin kwanaki 60. Sannan kuma, gwamnatin wucin gadi ta kasar za ta jefa kuri'ar raba gardama game da daftarin cikin kwanaki 30 masu zuwa, idan aka zartas da shi, Masar za ta gudanar da zaben majalisar dokoki cikin kwanaki 15 masu zuwa.(Bako)