A lokacin ziyarar tasa a Indonesia,Shugaba Xi zai gana da takwaransa Susilo Bambang Yudhoyono da kuma mataimakin Shugaban kasar Boedijono da shugabanni majalissar dokokin kasar sannan kuma zai halarci liyafar cin abinci da wasu manyan 'yan kasuwa.
Kasashen biyu sun cimma nasarori tare wajen hadin gwiwa a bangaren kimiyya da fasasha,ilimi,al'adun gargajiya,musanyan jama'ar su, tsaro da kariya, sufurin jiragen ruwa da na jiragen sama.
Bayan kammala ziyarar sa a Indonesia, Shugaba Xi zai ziyarci kasar Malaysia daga baya kuma ya sake komawa Indonesian domin halartar taron shugabannin kasashe membobin Kungiyar habaka tattalin arzikin nahiyar Asiya da yankin tekun Pacific wato APEC da za'a yi daga ranar 7 zuwa 8 ga watan na Oktoba. (Fatimah Jibril)