Shugabannin Sin sun ajiye kwandon furanni ga mutum-mutumin tunawa da jaruman jama'ar kasar Sin
Ranar 1 ga watan Oktoba, rana ce ta cika shekaru 64 da kafa Jamhuriyyar jama'ar kasar Sin. A safiyar wannan rana, a yayin da ake ruwan sama, Xi Jinping, Li Keqiang, Zhang Dejiang, Yu Zhengsheng, Liu Yunshan, Wang Qishan, Zhang Gaoli da sauran shugabannin JKS da na gwamnatin kasar Sin sun kai ziyara a filin Tian'anmen, inda suka ajiye kwandunan furanni ga mutum-mutumin tunawa da jaruman jama'ar kasar Sin tare da wakilan sassa daban daban na kasar, a kokarin nuna girmamawarsu ga jaruman jama'ar kasar.
Wannan ne karo na farko da sabbin shugabannin Sin suka ajiye kwandunan ga mutum-mutumin tunawa da jaruman. A safiyar wannan rana da misalin karfe 10, an kaddamar da wannan biki, inda shugabannin Sin suka tsaya karkashin laima daya, a cikin ruwan sama domin nuna ta'aziyyarsu.
Bana shekara ce ta hudu a jere da aka yi bikin ajiye kwandon furanni ga mutum-mutumin tunawa da jaruman jama'ar kasar Sin a ranar murnar kafa Jamhuriyar jama'ar kasar Sin. An lura da cewa, ko da yake ana ruwan sama sosai a lokacin bikin, amma hakan bai sa an fuskanci wani matsala ba a lokacin bikin.(Fatima)