in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasar Sin sun aike da sakon ta'aziya ga shugaban kasar Pakistan
2013-09-25 20:18:55 cri
A ranar Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da Firaministan kasar Sin Li Keqiang suka aikawa shugaban kasar Pakistan Mamnoon Hussain sakon ta'aziya, sakamakon mummunan girgizar kasar da ta halaka mutane da dama tare da asarar dukiyoyi ranar Talata a yankin kudu maso yammacin kasar.

Shugaba Xi ya ce kasashen Sin da Pakistan abokai ne da ke makwabtaka da juna, kuma a kullum a shirye suke wajen taimakawa juna, inda ya bayyana kudurin kasar Sin na baiwa kasar ta Pakistan dukkan taimakon da ya wajaba.

Shugaba Xi Jinping ya ce a madadin shi kansa, gwamnati da kuma al'ummar kasar Sin, yana mika sakon ta'aziya ga iyalan wadanda suka mutu da kuma jikkata a wannan bala'i.

Ya ce, ya gamsu cewa, karkashin jagorancin shugaban kasar da kuma gwamnatin Pakistan, al'ummar ta Pakistan za su hada kai don magance matsalolin da suka samu kansu a ciki sakamakon wannan bala'i kana su sake gina gidajensu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China