in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kasance abokiyar Afirka cikin ko wane irin yanayi, in ji shugaban kasar Sin
2013-03-30 16:22:22 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping yayin ziyarar da yake a nahiyar Afirka ya bayyana a ranar Jumma'a 29 ga wata cewa, kasar Sin za ta ci gaba da zama abokiya ga nahiyar cikin ko wane irin yanayi.

A cikin jawabin da ya gabatar yayin ziyara a kasar jamhuriyar Kongo, shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kiyaye akidar zaman lafiya, bunkasa, hadin gwiwa, moriyar juna da kuma sadaukar da kanta ga tabbatar da zaman lafiya a duk fadin duniya da kuma samun ci gaba na bai daya.

Ziyarar da ya kai a jamhuriyar Kongo ita ce takin karshe na ziyarar da shugaba Xi ya kai kasashe hudu, wacce ta kasance ziyararsa ta farko zuwa kasashen waje bayan hayewa kujerar shugaban kasar Sin a farkon wannan wata. Ya fara kai ziyara ne a kasashen Rasha, Tanzania da kuma Afirka ta Kudu.

A sabuwar alkiblar, kasar Sin za ta samar da dimbin dama na bunkasar Afirka kana ci gaban nahiyar zai samar da damar kara bunkasar kasar Sin, in ji shugaba Xi, inda ya yi kira ga bangarorin biyu da su dage kan akidar cin moriyar juna ta yin hadin gwiwa.

Ya ci gaba da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ba da goyon baya da tallafi ta moriyar juna ga kasashen Afirka, za ta ci gaba da ba da agaji iya kokarinta, fadada harkar cinikayya da zuba jari a nahiyar, bunkasa dangantaka da kuma yin hadin gwiwa a fuskar shawo kan kalubale na tattalin arzikin duniya da sauran matsaloli.

Ya kara da cewa, kasar Sin na mai nuna goyon baya ga kasashen Afirka su bi turbar bunkasa da su kaiwa kansu zabi wacce kuma ta dace da yanayinsu na gida kana tana mai ba da goyon baya ga yunkurin kasashen Afirka da kungiyoyin yankuna, kamar kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU, wajen samar da kariyar ikon mulkin kai da 'yancin warware matsalolin nahiyar da kansu.

Har wa yau, shugaban na Sin ya lura cewa, dankon zumuncin da ke tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin, wanda ya samo tushi daga jama'arsu, muhimmin tushe ne ga dangantakar dake tsakaninsu.

Ya yi kiran samar da karin hanyoyin ganawa kai tsaye tsakanin jama'ar Sin da Afirka da kuma samar da kafofin bayanai don fahimtar juna, a kokarin tabbatar da ganin abotar dake tsakaninsu ta kafu a zukatan jama'arsu domin manyan gobe.

Shugaba Xi ya kara da cewa, zai ci gaba da tunawa da wannan ziyarar da ya kawo Afirka tare da nuna imanin cewa, kawancen da ke tsakanin Sin da Afirka zai dore har abada kamar yadda ruwan kogin Yangtze da na Kongo ke ci gaba da gudana. (Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China