in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta shirya tura karin dakarun wanzar da zaman lafiya yankin Darfur
2013-01-05 15:49:08 cri
Rundunar sojojin Najeriya ta fada a ranar Jumma'a cewa, ta kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba na tura dakaru 800 yankin Darfur na kasar Sudan.

Wadannan dakarun sun kammala samun horo na tsawon makonni 4 a cibiyar sojan wanzar da zaman lafiya ta Najeriya da ke jihar Kaduna a arewa maso tsakiyar kasar

Kwamandan cibiyar, Manjo-Janar John Zaruwa ya bayyana cewa, shirin horaswar wani bangare ne na kokarin da sojojin ke yi na cusa kwarewa a aikin tura tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD zuwa sassan daban-daban na duniya.

Zaruwa ya shaidawa wadanda suka halarci shirin cewa, dakarun sun samu horon da ya dace ta yadda za su gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a yankin Sudan yadda ya kamata.

Dakarun Najeriya dai sun sha taka irin wannan rawa a baya a kasashen Jamhuriyar demokiradiyar Congo, Liberia, Saliyo da kuma Afirka ta kudu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China