Kwamitin mai mambobi 15 ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki kan wannan kuduri da su ci gaba da kokarin inganta tattaunawa ta siyasa a cikin kasar don a samu cimma kafa yanayin da ya dace na gudanar da zabe cikin adalci wanda kuma zai samu karbuwa ga dukkan jama'ar kasar domin a samu dawo da oda ta tsarin mulkin kasa gami da dorewa na tsawon lokaci a kasar.
Kwamitin ya yi nunin cewa ya damu matuka dangane da yanayi da ake ciki a kasar bayan juyin mulki na soji da aka yi a kasar a watan Aprilun shekarar da ta wuce wadda ya yi sanadin hargitsa shirin zabe aka tashi babu sakamako.
Ayyuka da aka damkawa ofishin kafa zaman lafiya a kasar Guinea-Bisau na MDD sun kunshi kawo inganci a cibiyoyi, kiyaye doka, ba da hadin kai ga shirin kawo sulhu da kuma taimakawa hukumomi a yaki da fataucin miyagun kwayoyi.
Kudurin na mai bayyana cewa babban sakataren MDD Ban Ki Moon zai ba da rahoto kan kasar Guinea-Bisau a ranar 30 ga watan Aprilun shekarar 2013 domin a tantance irin karin gudummawa da kasar ke bukata. (Lami Ali)