Sojojin injiniya da kasar Sin za ta tura su zuwa kasar Sudan ta kudu domin na kiyaye zaman lafiya sun yi rantsuwa
A yau 10 ga wata da safe ne, sojoji da hafsoshi 275 wadanda kasar Sin za ta tura su zuwa yankin Wawu na kasar Sudan ta kudu domin tabbatar da zaman lafiya a yankin suka yi rantsuwa. Wadannan sojojin injiyoyi za su tashi zuwa yankin Wawu a ran 15 ga wata, sannan wani karamin rukunin jinyya dake kunshe da mutane 63 zai isa yankin tare da su.
Nauyin da aka dora wa wadannan sojoji injijniya na kasar Sin shi ne gyara da shimfida hanyoyin mota, gadoji da filin tashi da saukar jiragen sama, tare da gyara injunan samar da ruwan sha da na samar da wutar lantarki, da lalata harsassai da makamai, har ma za su ba da taimako ga sauran rundunonin tabbatar da zaman lafiya a kasar Sudan ta kudu idan akwai bukata. Wa'adin aiki nasu a kasar Sudan ta kudu zai kai tsawon watanni 8. (Sanusi Chen)