A yammacin ranar 13 ga wata, rundunar kiyaye zaman lafiya karo na farko da Sin ta tura kasar Sudan ta kudu, ta dawo nan kasar Sin bayan da ta kammala wa'adin aikin ta na tsawon shekara daya.
Bisa bukatar MDD, a ranar 11 ga watan Nuwambar shekarar 2011, ma'aikatar ba da tsaro ga jama'a ta kasar Sin, ta tura wata rundunar kiyaye zaman lafiya ta farko yankin da MDD ke ba da kulawa a kasar Sudan ta kudu. Wannan runduna ta kunshi 'yan sanda 14. Bayan sun isa yankin, sun fuskanci kalubaloli da dama, amma duk da hakan sun taimakawa kasar wajen tabbatar da halin da ake ciki na wucin gadi, sun kuma ba da taimako ga 'yan sanda wuri tabbatar da bin doka da oda, da kuma yin kwaskwarima da sake kafa hukumar gudanar da doka da shari'a. Rundunar dai ta kammala aikinta yadda ya kamata, al'amarin da ya kafa siffar 'yan sandan kasar Sin a duniya.
An ce, a ran 12 ga watan Satumba na shekarar bana, yayin bikin bada lambobin yabo da tawagar musamman ta MDD dake Sudan ta kudu ta yi a Jubba, hedkwatar kasar, an baiwa rundunar kasar Sin lambar yabo ta "Samar da zaman lafiya", ta MDD. (Amina)