A watan Yuli na shekarar bara, 'yan sanda 17 daga ofishin 'yan sanda na lardin Hunan, kwalejin 'yan sanda na lardin, ofisoshin 'yan sanda na biranen Changsha, Zhuzhou, Xiangtan da sauran biranen lardin sun je kasar Liberia don gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya. Yawan shekarunsu a takaice ya kai 35. Guda 9 daga cikin 'yan sandan sun yi aiki a Monrovia, babban birnin kasar Liberia, kana guda 8 sun yi aiki a sauran sassan kasar. Bisa labarin da aka bayar, an ce, rukunin 'yan sanda na lardin Hunan shi ne rukuni na 10 da kasar Sin ta tura zuwa kasar Liberia don yin aikin kiyaye zaman lafiya. Yayin da suke gudanar da aikinsu, an yi zaben shugaban kasar Liberia. (Zainab)