A cewar minista Camara, da ma ba a taba shirin girke sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar ba, domin ba a san karfin da masu tsattsauran ra'ayin addini suke da shi ba. Wannan dalili ne ya sanya aka yi taruruka da yawa kafin a tura sojojin kasa da kasa masu tallafawa kasar Mali na MISMA.
Sai dai ya ce a ganinsa, duk da cewa kasashen kungiyar ECOWAS sun tura sojoji zuwa kasar Mali, amma ba za a samu damar cimma buri ba cikin sauri in ba tare da tallafi daga wata kasa mai karfi kamar Faransa ba.(Bello Wang)