in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta kawo karshen aikin da ta yi a kasar Sham na kiyaye zaman lafiya
2012-08-25 19:23:38 cri

Ranar 19 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya yanke shawarar kawo karshen aikinsa a kasar Sham na kiyaye zaman lafiya na tsawon kwanaki 120. Masu sa ido na kasar Sin gudu hudu sun iso birnin Beijing a ranar 25 ga wata.

A ran 21 ga watan Afrilu, MDD ta zartas da kuduri mai lamba 2043, inda aka yanke shawarar tura wata tawaga zuwa kasar Sham dake kunshe da 'yan kallo na sojada wasu masu sa ido kai harkokin jama'a 300, domin gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya. Bisa bukatun MDD, Sin ta tura 'yan kallo jami'an soja 9.

Masu sa ido na kasar Sin sun bi ka'idar tsarin mulkin MDD yadda ya kamata bayan sun isa kasar Sham, wadanda kuma suka tinkari kalubaloli da dama, ciki har da rikicin da ya barke a Damascus babban birnin kasar. Duk da haka, sun gudanar da aikinsu yadda ya kamata tare da samun amincewa daga tawagar sa ido ta MDD da ma kasashe daban-daban.

Wani jami'i na ofishin kula da ayyukan kiyaye zaman lafiya na kasar Sin ya ce, a matsayin mamba na dindindin na kwamitin sulhu na MDD, Sin za ta ci gaba da shiga ayyukan da MDD ta yi wajen kiyaye zaman lafiya domin ba da taimakonta. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China