Shugaban ofishin 'yan sanda na jihar Guangxi Liang Shengli ya ce, hukumar 'yan sanda ta jihar Guangxi ta kafa wannan rukunin kiyaye zaman lafiya da zai je kasar Sudan ta kudu a madadin 'yan sandan kasar Sin, kuma wannan aiki ya zama muhimmin aikin siyasa da ke bi manufofin harkokin waje da Sin ta tsara da kuma kiyaye zaman lafiya a duniya. Jihar Guangxi jihar farko ce ta kananan kabilu da ta kafa rukunin 'yan sandan kiyaye zaman lafiya da kanta.
'Yan sanda 13 dake cikin rukunin 'yan sanda na biyu na kasar Sin sun taba yin aiki a cikin hukumomin yaki da ta'addanci, kwastam, yin sintiri, yin bincike a iyakar kasa da kasa da dai sauransu. Tun daga shekarar 2000, jihar Guangxi ta riga ta tura 'yan sandan kiyaye zaman lafiya 12 zuwa East Timor, Haiti, Liberia da sauran yankuna don gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya. (Zainab)