Binciken da cibiyar shawo kan kwararowar hamada ta Gansu ta gudanar a Tarayyar Najeriya ya sheda cewa, yadda yawan al'ummar kasar ke karuwa cikin sauri a shekarun baya, ya sa an mai da dimbin filayen ciyayi a matsayin gonaki, kana a filin ciyayi da ya rage a kan yi kiwon dabbobi kansa, lamarin da ke janyo zaizayewar kasa idan iska na bugawa cikin lokacin rani, hakan na zama sanadiyyar karin saurin kwararowar hamada.
Game da haka, Liu ya yi alkawarin cewa, shi da masanan cibiyarsa za su tallafa wa kasar Najeriya da fasahohi, don kara karfinta wajen kula da kwararowar hamada da yin amfani da rairayi. Kana ya ce ban da Najeriya, za su aiwatar da aikin tallafi a sauran wasu kasashen Afirka wadanda su ma suke fuskantar matsalar kwararowar hamada, kamarsu Kenya,Masar, Aljeriya, Nijar, da dai makamantansu.
An ce, kasashen Afirka a nasu bangare suna fatan ganin fasahohi da kudin da gwamnatin kasar Sin take samarwa domin magance kwararowar hamada a kasashen, kana suna fata kasar Sin za ta kara mara musu baya da wasu fasahohin da suka hada da dasa itatuwa, tsimin ruwa, kare filayen ciyayi, da dai makamanta, ta yadda za su iya samun damar hana kwararowar hamada, da kawar da talauci.(Bello Wang)