Kwanan baya a nan birnin Beijing, an gabatar da ajin horar da masanan yaki da kwararowar hamada bisa tsarin dandalin tattaunawa kan samun hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika. Gwanayen 'yan kasar Sin a wannan fanni sun horar da jami'ai sama da 30 na gwamnatocin kasashe 13 ciki har da Aljeriya, Camaroun, Ruwanda.
Babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya aika da wasikar nuna kyakkyawar fata tare da yabawa ci gaban da Sin ta samu a fannin yaki da kwararowar hamada. Wakilan hukumar kiyaye muhalli na MDD da hukumar abinci da aikin gona ta MDD, da wakilan ofisoshin jakadancin kasa da kasa sun halarci bikin bude ajin.(Amina)