An bude taron (COP11) karo na 11 na kwamitin MDD kan yaki da hamada (UNCCD) a ranar Litinin a birnin Windhoek na kasar Namibia, wakilan dake halarta wannan taro za su tattauna hanyoyin da za'a cimma wajen fuskantar hamada da zaizayewar kasa. Kimanin mahalarta dubu biyu zuwa dubu uku suke wakiltar bangarori 195, kungiyoyin MDD, kungiyoyin gwamnatoci da masu zaman kansu da kungiyoyin fararen hula suna halartar wannan taro na COP11 bisa manufar yin shawarwari da bullo da hanyoyin da za su taimaka wajen kyautata yanayin zaman rayuwar al'ummomin yankunan dake fama da fari, daidaitawa da farfado kasa domin samun amfanin noma, ta yadda za'a iyar rage radadin kalubalen hamada.
A cikin jawabinsa a yayin bude taro, ministan muhallin kasar Namibia Uahekua Herunga ya bayyana cewa lalacewar kasa, babbar barazana ce kan kokarin da ake na samun cigaba. Wannan taro zai dogaro ga tsarin da aka cimma a taron COP10 da kuma sakamakon taron Rio+20 domin tsai da matakan jan birki da wannan matsaloli, da kuma bullo da dabarar UNCCD da bangarorin da abin shafa domin karfafa dabarun rage lalacewar kasa a fadin duniya, in ji mista Herunga. A nasa bangare, sakataren kwamitin UNCCD, mista Luc Gnacadja ya yi kira da hada karfi tare domin fitar da wani tsarin magance matsalar hamada da zaizayewar kasa.
A cewar MDD, lalacewar kasa, matsala ce dake shafar mutane biliyan 1,5 a duniya da kuma janyo talauci a duniya. (Maman Ada)