Yayin da ya halarci taron bincike kan bunkasa gonaki a wasu yankunan da ke lardin Gansu, wani masanin kasar Rasha mai suna Zon ya nuna cewa,za a yi amfani da hasken rana da ruwa kalilan wajen aikin raya gonakin da ke Hamada, watau aiki ne da ba ya bukatar albarkatu da yawa. Bugu da kari, wani masanin hamada wanda ya zo daga kasar Isra'ila mai suna Orlovsky yana ganin cewa, fasahar raya aikin gona a cikin hamada da ake yi a lardin Gansu shi ne ke kan gaba a duniya, wadda za ta zama abin koyi ga kasa da kasa. (Maryam)