Yayin da ake bikin ranar hana kwararowar hamadam da rani na duniya karo na 18 a ran 17 ga wata, an kaddamar da wani taron bita kan manufofi da kimiyyar hana kwararowar hamadam a nan birnin Beijing, jami'an kasashe fiye da 20 na Afirka sun shiga aikin yin bicike don hana kwararowar hamada.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a lokacin wannan taron bitan na tsawon makonni uku, masana a wannan fanni kimanin 20 za su ba da bayyani kan tsare-tsaren da Sin ta dauka wajen hana kwararowar hamada a fannoni daban-daban ciki har da manufofi da dokoki, taimako a fannin aikin kudi, tsare-tsare, kimiyyar hana kwararowar hamada da bunkasuwar sana'o'in da suka shafi wannan aiki. Haka kuma, mahalarta taron da suka fito daga kasashen Afrika zasu yi musayar ra'ayi kan wasu matakai masu amfani ta hanyar kai rangadi da yin shawarwari.
Sin ta kasance daya daga cikin kasashen da suke fi fama da kwararowar hamadam a duniya. Yawan yankunan da hamadam ya shafi a kasar Sin ya kai kashi 3 bisa 10. Yanzu Sin ta sami ci gaba mai kyau wajen yaki da kwararowar hamada bisa kokarin da ta yi, kasashen duniya kuma sun gamsu da nasarar da Sin ta samu.
A watan Yuni na shekarar 2006 a nan birnin Beijing, Sin da kasashen Afrika sun kira taron koli na dandalin tattaunawar hadin kai tsakaninsu, inda suka shigo da aikin hana kwararowar Hamada cikin tsarin Beijing a dandalin.(Amina)