A gun taron manema labaru da aka yi a birnin Beijing, Zhu Lieke ya ce, a 'yan shekarun nan, gwamnatin kasar Sin ta dauki wasu manyan matakai domin magance wannan matsala, su ma jama'ar da suke fama da kwararowar hamada da rairayi suna yi iyakacin kokari, hakan ya sa an cimma nasara sosai a wannan fanni. Kafin karshen shekarar 2009, yawan yankunan dake fama da kwararowar hamada ya kai murabba'in kilomita miliyan 2.62, yayin da yankunan dake fama da rairayi ya kai murabba'in kilomita miliyan 1.73 wanda ya kai kashi 27 cikin 100 da kashi 18 cikin 100 bisa na dukkan fadin kasar, kuma ya ragu sosai bisa na makamancin lokaci na shekarar 2004.(Amina)