Francois Hollande wanda ya lashe zaben shugaban kasar Faransa ya jaddada a ran 7 ga wata cewa, kasarsa tana dora muhimmanci sosai kan tasirin da kasar Sin ta yi a fannonin siyasa da tattalin arziki na kasa da kasa, yana fatan kasashen biyu za su ci gaba da samun sakamako mai kyau wajen yin hadin gwiwar sada zumunta.
Francois Hollande ya gana da jakadan kasar Sin dake kasar Faransa Kong Quan a wannan rana a birnin Paris, inda ya ce, kasar Faransa tana son ci gaba da ingiza hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki a tsakanin kasashen biyu, domin kara zuba jari tsakaninsu. Ya kamata kasashen biyu su ci gaba da karfafa hadin gwiwarsu a cikin kungiyar G20 da sauran muhimman batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya.
A yayin ganawar, Mr. Kong Quan ya mika wa Francois Hollande sakon taya murna daga shugaban kasar Sin Hu Jintao. Francois Hollande ya karanta wannan sako tare da nuna godiya sosai ga shugaba Hu.
Francois Hollande ya lashe zaben da aka yi zagaye na biyu a ranar 6 ga wata, kuma zai yi ranstuwar kama aiki a ran 15 ga wata. Jakadan kasar Sin Kong Quan ya kasance jakada na farko na kasashen waje da Francois Hollande ya gana da shi bayan lashe zabensa.(Lami)