in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama da Romney na ci gaba da yakin neman zabe bayan mahaukaciyar guguwar Sandy
2012-11-02 17:01:44 cri
Bayan da aka farfado da harkokin yau da kullum a wasu jihohin kasar bayan wucewar mahaukaciyar guguwar Sandy a gabashin mashigin tekun kasar Amurka, shugaban kasar Amurka Barack Obama da abokin takararsa Willard Mitt Romney sun koma fagen yakin neman zaben shugaban kasar na bana domin kara samun goyon bayan jama'a kafin zaben a ranar 6 ga wata.

Obama ya tafiyar da yakin neman zabensa a Green Bay dake jihar Wisconsin, Las Vegas dake jihar Nevada da kuma Denver dake jihar Colorado a wannan rana. A yayin da yake jagorantar wani taro a Green Bay, Obama ya bayyana cewa, kasar Amurka tana samun farfadowa a fannin tattalin arziki a karkashin jagorancinsa. Ya bayyana ayyukansa kan kwaskwarimar inshorar kiwon lafiya, sa ido kan wall street da dai sauransu. Hakazalika, Obama ya zargi Romney da yunkurin gudanar da matakan da za su kawo illa ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Amurka.

Kamar Obama, Romney shi ma ya tafiyar da nasa yakin neman zabe a jihar Virginia. A gun taron da aka gudanar a birnin Roanoke dake jihar, Romney ya zargi Obama da rashin taimakawa kasar Amurka wajen kawar da matsalar tattalin arziki a shekaru 4 da suka wuce. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China