A cikin wata sanarwa, ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce, gwamnatin kasar ta samarwa kungiyar adawa wadannan kudaden ne domin taimaka mata wajen kyautata zaman rayuwar jama'a da aikin ba da agaji. Sanarwa ta ce, za a yi amfani da wadannan kudade domin sake gina wasu manyan ayyukan more rayuwa da aka lalata lokacin yakin basasa da kuma samarwa jama'ar Libya jiyya da abinci.(Amina)