Bisa sakamakon kididdigar da hukumar ta samar, an ce, yawan kuri'un da Hugo Chavez ya samu ya kai kashi 54.42 cikin dari daga cikin kashi 90 cikin dari na kuri'un da aka kidaya, yayin da 'dan takarar jamiyyar adawa, Henrique Capriles ya sami kashi 44.97 cikin dari.
Daga bisani ne kuma, Hugo Chavez ya nuna godiyarsa matuka, ga dukkan jama'ar da suka jefa kuri'a a lokacin zaben, gami da daukacin magoya bayansa, har ma da wadanda ba su zabe shi ba.
Bugu da kari, Mr. Chavez ya jinjinawa shugaban jamiyyar adawan, saboda yarda da ya yi da sakamakon babban zaben.
Tun lokacin da Hugo Chavez ya fara rike da mulkin kasar ta Venezuela a shekarar 1998, kawo yanzu, shekaru 14 ke nan. Yanzu dai, Mr. Chavez zai ci gaba da wa'adin aikinsa na shugaban kasar na tsawon shekaru 6 a nan gaba sakamakon nasarar da ya samu a wannan babban zaben.(Maryam)