An zabi Francois Hollande shugaban kasar a Faransa ya kuma yi alkawarin bauta ma kasar
Francois Hollande, dan takarar shugabancin kasar Faransa a shekara ta 2012 a karkashin jama'iyyar 'yan gurguzu, ya kasance sabon zababben shugaban kasar da kashi 51.24 cikin 100 na kuri'un da aka tabbatar da sahihancinsu, kamar yadda sakamakon da ma'aikatar cikin gida ta kasar ta baiyyana a yammacin ranar Lahadi a karfe 10 da muti 10.
Jim kadan bayan bayyana sakamakon zaben, a Tulle, Francois Hollande ya yi kalamin cewa, "A wannan rana ta 6 ga watan Mayu, al'ummar kasar Faransa sun zabo canji."
1 2