A ranar 10 ga wannan wata, kwamitin tsarin mulkin kasar Faransa ya gabatar da sakamakon zaben shugaban kasar a zagaye na biyu a hukunce, Francois Hollande, dan takara na jam'iyyar gurguzu ta kasar ya samu yawancin kuri'un da aka jefa, a gaban shugaba Nicolas Sarkozy.
Bisa sakamakon zaben da kwamitin tsarin mulkin kasar Faransa ya gabatar, an ce, a zaben shugaban kasar a zagaye na biyu da aka gudanar a ranar 6 ga wannan wata, an jefa kuri'u kimanin miliyan 34.86, a cikinsu Hollande ya samu kuri'u miliyan 18, wanda ya kai kashi 51.64 cikin kashi dari na dukkan kuri'un da aka jefa, kuma ya zarce yawan kuri'un da ake bukata wato miliyan 17.43.
Bisa tsarin mulkin kasar Faransa, an zabi sabon shugaban kasar ta hanyar jefa kuri'u.
Idan babu wanda ya samu rinjayen kuri'u a zagayen farko, 'yan takara biyu da suka fi samun kuri'un a zagayen farko su zasu fafatawa shiga a zagaye na biyu.
A ranar 10 ga wannan wata, firaministan kasar Faransa François Fillon ya gabatar da takardar yin murabus ta gwamnatinsa ga shugaban kasar na yanzu Nicolas Sarkozy.(Zainab)