An fara jefa kuri'u a yawancin jihohin kasar Amurka daga safe zuwa dare na ranar 6, kuma za a zabi sabon shugaban kasar karo na 57 daga cikin 'yan takara biyu wato shugaban kasar na yanzu Barack Obama da kuma tsohon gwamnan jihar Massachusetts Willard Mitt Romney. Za a gabatar da sakamakon binciken ra'ayoyin masu jefa kuri'a a daddaren wannan rana.
Bisa kididdigar da aka yi game da ra'ayoyin jama'ar kasar Amurka, an ce, goyon baya da 'yan takaran biyu ke samu ya yi daidai da juna, a ganin masanan kasar Amurka, ba za a iya yin hasashe game da sakamakon zaben shugaban kasar ba. Sabo da haka, wasu jihohin da ba su tabbatar da nuna goyon baya ga ko wane dan takara ba, za su yi babban tasiri ga sakamakon zaben a wannan karo. (Zainab)