Wadannan kasashen biyar za su karbi jagoranci daga hannayen kasashen Colombia, Jamus, India, Portugal da Afirka ta Kudu kuma za su soma aiki daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2013 har zuwa ranar 31 ga watan Disamban shekara ta 2014. Sauran mambobin kwamitin sulhu na MDD da ba na din din din ba guda biyar su ne kasashen Azerbaijan, Guatemala, Morocco, Pakistan da Togo wadanda suka samu wannan matsayi cikin shekara ta 2011, kuma wa'adin aikinsu zai kare a kashen shekara ta 2013.(Maryam)