in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Kenya na barazanar korar malaman makarantar dake yajin aiki
2013-07-16 10:08:15 cri
Takkadama tsakanin gwamnatin kasar Kenya da bangaren malaman makaranta na kasar, ta kai ga sanya gwamnatin Kenya fitar da wata barazana a ranar Litinin ta sallamar duk wasu malaman makarantar dake yajin aiki, idan har ba su amince da koma wa aiki ba tun daga bakin ranar Talata, a lokacin da malaman makarantar suke shiga mako na hudu cikin yajin aiki na gama gari, lamarin da ya gurguntar da aikin bada ilmi a cikin makarantun gwamnati fiye da dubu goma. Magatakardan kasar a fannin bada ilmi, forfesa Jacob Kaimenyi ya bayyana cewa, gwamnati ba zata cigaba ba da rufe ido kan rashin da'a daga wajen malaman makaranta ba da har yanzu suke cigaba da bijirewa koma wa aiki, duk da wani kudurin shari'a na bin doka da aka fitar . (Maman Ada)

 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China