A yayin ganawar, Zhang Baowen ya isar wa shugaba Kenyatta da sakon murna da gaisuwa daga wajen shugaba Xi Jinping, tare da taya shi murnar samun nasarar gudanar da babban zabe a Kenya. A cewarsa, kasar Sin ta darajta dankon zumuncin da ke tsakaninta da Kenya, kuma tana son yin amfani da damar cika shekaru 50 da kulla dangantakar diplomsiyya a tsakanin kasashen 2 wajen hada kai da Kenya, a kokarin habaka da inganta mu'amala da hadin gwiwa a tsakaninsu a sassa daban daban, sabo da haka za a kara raya dangantakarsu zuwa sabon mataki.
A nasa bangaren kuma, shugaba Uhuru Kenyatta ya gode wa takwaransa na kasar Sin Xi Jinping da ya aika da manzon musamman don halartar bikin rantsar da shi, a ganinsa, lamarin da ya kasance tamkar babban yabo ne ga gwamnatin Kenya da jama'ar kasar. Haka kuma, sabon shugaban na Kenya ya ce, sabuwar gwamnatin kasar za ta himmantu wajen zurfafa hadin gwiwar abokantaka a tsakanin kasashen 2, da kyautata mu'amala a tsakanin shugabanninsu, gwamnatocinsu da jam'iyyunsu, da kuma inganta hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya, muhimman ayyukan more rayuwar jama'a, aikin gona da dai sauransu. (Tasallah)