Ranar 9 ga wata, Uhuru Kenyatta wanda ya lashe zaben zama shugaban Kenya ya yi rantsuwar kama aikinsa a birnin Nairobi hedkwatar kasar, ke nan ya zama shugaba na hudu tun bayan da kasar ta samu 'yancin kai.
A cikin jawabinsa, Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa a cikin wa'adinsa na shekaru biyar, zai yi kokarin cika al'akwarin da ya yi wa jama'ar Kenya ta hanyar samar da guraben aikin yi da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki, tare kuma da kara zuba jari ga sha'anin ba da ilmi, ba da jiyya, sha'anin noma da sauransu. A sa'i daya kuma, sabon shugaban kasar Kenya cewa ya yi zai kara hadin gwiwa da kasashe dake makwabtaka da kasar Kenya a kokarin sa kaimi dunkulewar tattalin arzikin Afrika.
Uhuru Kenyatta dai ya lashe zaben shugaban kasar Kenya da aka yi a ran 4 ga watan Maris bisa yawan kuri'un da ya samu na kashi 50.07 bisa dari. (Amina)