in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gobara ta tashi a filin saukar jiragen sama na kasar Kenya
2013-08-07 15:55:40 cri

A safiyar ranar 7 ga wata bisa agogon wurin, gobara ta tashi a filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Jomo Kenyatta dake birnin Nairobi hedkwatar kasar Kenya. A yanzu haka dai an rufe filin sakamakon tashin gobarar.

Hukumar kula da harkokin filin saukar jiragen sama ta bayyana a shafin Intanet dinta cewa, ana kai fasinjoji yankin dake cikin yanayi mai kyau saboda yadda gobarar ta yi tsanani.

Ya zuwa yanzu, ma'aikatan kwana-kwana sun je wuri don kokarin kashe wutar. Ministan zirga-zirga da manyan ababen more rayuwa Michael Kamau ya ce, ana bincike don gano dalilin aukuwar hadarin, kuma zuwa yanzu babu wani labari kan asarar rayuka.

An ba da labari cewa, wannan filin saukar jiragen sama ya kasance fili mafi girma a kasar Kenya, kuma ya kasance mahadar hanyoyin jiragen sama a gabashin nahiyar Afrika, wanda ke karbar jiragen sama kasashe daban-daban wadanda za su wuce. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China